Saudiya ta ce kuskure ne harin da ta kai wa fararen hula a Yemen
Rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta, ta dauki alhakin harin da jiragen yaki suka kai a birnin Sana’a wanda ya hallaka fararen hula 14 ciki harda kananan yara.
Wallafawa ranar:
Sai dai kakakin rundunar hadakar Kanal Turki al-Malki, ya ce, an samu kkuskure ne na na’ura ba wai da niyya aka farwa fararen hular ba.
Al-Malki ya bayyana nadamar rundunar tare da yi wa iyalan wadanda harin ya ritsa da su ta’aziyya.
Kakakin ya kuma zargi mayakan Houthi mabiya mazhabar Shi’a da kafa bariki hadi da cibiyar yada sakwanni a kusa da gidajen fararen hula.
Tun a shekara ta 2014 yankin ke karkashin mayakan Houthi bayan korar sojin gwamnatin kasar ta Yemen da suka yi a waccan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu