rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Pakistan Myanmar Bangladesh Malaysia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi zanga-zangar goyon bayan Musulman Myanmar

media
Wasu daga cikin Musulman Rohingya da ke neman mafaka a Bangladesh 路透社。

Dubban mutane sun fito zanga-zanga a Pakistan da Malaysia a yau Juma’a domin nuna  adawa da kisan Musulmin Rohingya a Myanmar wadanda ke ci gaba da tserewa zuwa Bangladesh.


Masu zanga-zangar sun fito suna daga kwali mai dauke da sakon da ke alla-wadai da shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi.

Suu Kyi da ta samu lambar yabo ta zaman lafiya a duniya na ci gaba fuskantar suka kan yadda ta ki fitowa fili ta soki yadda ake kisan mutanen na Rohingya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 1000 jami’an tsaron Myanmar suka kashe, yayin da sama da dubu dari uku suka fice zuwa Bangladesh don neman mafaka.