Isa ga babban shafi
Saudi-Qatar

Saudiya ta soke duk wata tattaunawa da Qatar

Saudiya ta soke gudanar da duk wata tattaunawa da Qatar, bayan a karon farko Sarakunan kasashen biyu sun zanta a jiya kan yadda za su warware sabanin da ke tsakaninsu.

Yariman Saudiya Muhammad Bin Salman, tare da Sarkin Qatar Tamim ben Hamad al-Thani, a wani taro a Doha
Yariman Saudiya Muhammad Bin Salman, tare da Sarkin Qatar Tamim ben Hamad al-Thani, a wani taro a Doha BANDAR AL-JALOUD / Saudi Royal Palace / AFP
Talla

Sarkin Qatar Tamim Bin Hamad al Thani ya zanta ta wayar tarho da Yariman Saudiya mai jiran gado Muhammad bin Salman kan yadda za a warware sabanin da ke tsakaninsu.

Saudiya ta zargi Qatar da kara gishiri kan asalin wanda ya bukaci a yi tattaunawar.

Tattaunawar ta watse ne bayan Saudiya ta zargi wasu kafofin yada labaran Qatar da yada cewa Saudiya ce ta bukaci a yi tattaunawar.

A watan Yuni ne Saudiya da kawayenta manyan kasashen Larabawa suka katse hulda da makwabciyarsu Qatar kan zarginta da taimakawa ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.