Isa ga babban shafi
Myanmar

'Yan tawayen Rohingya sun tsagaita wuta tsawon wata daya

Kungiyar ‘Yan tawayen kabilar Rohingya wato ARSA, ta sanar da tsagaita wuta na tsawon wata guda, tsakaninta da sojin kasar Myanmar, amma daga bangarenta kawai.

'Yangudun hijirar kabilar Rohingya yayinda suke hawa tsaunuka bayan ketarawa cikin kasar Bangladesh.
'Yangudun hijirar kabilar Rohingya yayinda suke hawa tsaunuka bayan ketarawa cikin kasar Bangladesh. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

‘Yan tawayen sun ce sun dauki matakin ne, domin bai wa jami’an agaji damar taimakawa, dubban ‘yan Kabilar ta Rohingya basa samun abinci, a arewa maso yammacin asar ta Myanmar.

Matakin 'yan tawayen ya zo ne, bayanda kungiyar bada agaji ta Red Cross, ta tura karin jami’anta zuwa arewa maso yammacin kasar, inda al’amura suka yamutse, sakamakon barkewar sabon ricikin da ya tilastawa dubban ‘yan kabilar Rohingya tserewa.

Red Cross ta tura karin jami'an sakamakon matakin da majalisar dinkin duniya ta dauka, na janye jami’anta daga yankunan kasar da ke fama da rikici, bayan zarginta da gwamnatin Myanmar ta yi, cewa tana goyon bayan ‘yan tada kayar bayan.

Zuwa yanzu akalla ‘yan kabilar Rohingya dubu 300,000 ne suka tsere zuwa Bangladesh, yayinda wasu 30,000, suka rasa matsugunnansu a cikin kasar, tun bayan yakin da sojoji suka kaddamar da yaki, kan kungiyar ‘yan tawayen kabilar ta Rohingya wato ARSA, wadda ta yi ikirarin kaiwa cibiyoyin ‘yan sandan kasar 30 hare-hare a cikin watan Agustan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.