Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Babu wanda ya isa hana mu mallakar makamin nukiliya - Jong-un

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong-un, ya ce babu wanda ya isa ya hana kasarsa cigaba da aikinta na mallakar makaman nukiliya, wadanda suke gudanar da gwajinsu a baya-bayannan.

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un tare da sauran mukarraban gwamnatinsa yayin duba wasu daga cikin manyan makamai masu linzamin da kasar ta mallaka.
Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un tare da sauran mukarraban gwamnatinsa yayin duba wasu daga cikin manyan makamai masu linzamin da kasar ta mallaka. KCNA via REUTERS
Talla

Kim Jong-un na maida martini ne dangane da kakabawa kasarsa Karin takunkuman karya tattalin arziki da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince tare da tabbatar da shi a jiya.

Ma’aikatar harkokin wajen Korea ta Arewa ta bayyana matakin kwamitin tsaron a matsayin shisshigi ga hakkin kasar na ikon kare kanta daga dukkanin barazanar tsaro, da kuma yunkurin jefa al’ummar kasar cikin mayuwacin hali ma haddasa musu koma bayan tattalin arzikin kasa.

Daga cikin manyan takunkuman karya tattalin arzikin da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniyar ya kakabawa Korea ta Arewan akwai, haramta mata saida kayayyaakin da masakunta suka sarrafa zuwa kasashen ketare, sai kuma hana kasar fitar da danyen manta kasuwar duniya.

Matakin, ya biyo bayan gwajin makamin nukiliya, mai dauke da sinadarin Hydrogen, da Korea ta Arewan ta yi a farkon Satumba, wanda ya haddasa motsawar kasa da karfin maki 6.3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.