rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Bangladesh Myanmar Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bangladesh ta gargadi sojin Myanmar kan keta mata iyaka

media
Wata 'yar gudun hijira 'yar kabilar rohingya Musulmi, yayinda take yiwa danta fifita a sansanin wucin gadin da suka kafa kan dutse bayan tserewa daga Mynamar zuwa Bangladesh. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain

Kasar Bangladesh, ta zargi gwamnatin Myanmar da saba ka’ida wajen keta mata iyakar sararin samaniya, tare da yin gargadin cewa muddin kasar ta Myanmmar ta maimaita hakan, zata maida mata martanin da ba zata ji dadinsa ba.


Gargadin na Bangladesh ya zo a daidai lokacin da dangantaka ke kara yin tsami tsakanin kasashen biyu, a dalilin cigaba da kwararowar Musulmi ‘yan kabilar Rohingya sama da 400,000 daga yammacin kasar ta Myanmar zuwa Bangladesh, domin gujewa kisan da sojin kasar ke wa fararen hula da sunan kokarin murkushe ‘ya’yan kungiyar ARSA masu dauke da makamai.

Rundunar sojin Bangladesh ta ce sau uku jirage masu saukar ungulu da kuma jirage marasa matuka na Myanmar, ke keta musu iyaka a ranar 10, 12 da kuma 14 ga watan Satumban da muke ciki.