Isa ga babban shafi
Iraqi

Majalisar yankin Kurdawa ta goyi bayan ballewa daga Iraqi

Majalisar shiyyar Kurdawa a Iraqi, ta goyi bayan kada kuri’ar raba gardama kan neman ‘yancin ballewa daga kasar.

Zauren majalisar yankin Kurdawa na Iraqi.
Zauren majalisar yankin Kurdawa na Iraqi. REUTERS/Azad Lashkari
Talla

Majalisar ta cimma matsayar amincewa da a kada kuri’ar a ranar 25 ga Watan Satumba da muke ciki, a zaman da ta yi karo na farko cikin shekaru 2, jiya Juma’a.

Matakin na zuwa bayanda a ranar Talatar da ta gabata, gwamnatin Iraqi ta bayyana, yunkurin a matsayin abinda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Suma dai kasashen Iran, Turkiya da Amurka basa goyon bayan bukatar ballewar yankin Kurdawan, tare da gargadin cewa hakan ka ‘iya raunana kokarin da ake na kakkabe ragowar mayakan IS daga gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.