rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Myanmar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

MDD zata ziyarci jihar Rakhine na Myanmar

media
Al'ummar Rohingya na cikin matsanancin hali a Bangladesh REUTERS/Mohammad Ponir Hossain

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yau ake saran jami’an ta su ziyarci Jihar Rakhine da aka samu kisan kare dangi kan ‘Yan Kabilar Rohingya a karon farko bayan tashin hankalin da aka samu.


Kakakin Majalisar Stephane Dujarric ya ce jami’an gwamnatin Myanmar ne zasu shirya ziyarar wanda zai bai wa Majalisar Dinkin Duniya ganin abinda ya faru.

Dujjaric ya ce ziyarar zata kunshi manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya.