Yarjejeniyar sulhu tsakanin Hamas da Fatah
Yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma bayan Masar ta shiga tsakaninsu, ta kunshi cewa kungiyar Fatah da ke da rinjaye a hukumomin Falasdinu sannan kuma ke zaune a gabar Yammacin Kogin Jordan, za ta karbi ikon tafiyar da yankin Gaza nan da ranar 1 ga watan Disamba.
Wallafawa ranar:
A shekarar 2007 ne aka fatattaki mahukumomin daga Gaza, amma a cikin watan jiya ne Hamas ta amince ta mika ma ta mulkin fararen hular yankin.
A cewar yarjejeniyar, bangarori da dama da ke hammaya da juna a Falasdinu da suka hada da Hamas da Fatah, za su gana a ranar 21 ga watan Nuwamba mai zuwa a birnin Al-Kahira na Masar don tattauna kan samar da gwamnatin hadaka.
Kazalika, za a mika kan iyakar Gaza da Isra’ila da Masar ga hukumomin Falasdinu nan da makwanni masu zuwa.
Har ila yau, yarjejniyar ta ce, shugaban Falasdinu Mahmud Abbas zai ziyarci Gaza a karon farko cikin shekaru 10 nan da kwanaki kalilan.
Sannan kuma nan da watan Fabairun 2018 ne, ake sa-ran warware matsalar dubban mutanen gwamnati da Hamas ta dauka aiki.
Kana, za a samar da sausauci dangane da tsauraran matakai da hukumomin Falasdinu suka dauka a Gaza, cikinsu har da batun kudin da mazauna yankin ke biya don samun makamashi.
Sai dai har yanzu, akwai sauran wasu batutuwa da bangarorin biyu ba su cimma matsaya a kansu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu