Isa ga babban shafi
Myanmar

Sojin Myanmar na binciken rikicin Rohingya

Rundunar sojin Myanmar ta bayyana cewa, tana gudanar da bincike don sanin irin rawar da jami’anta suka taka a rikicin jihar Rakhine da ya tilasta wa mutanen Rohingya tserewa zuwa Bangladesh.

Shugaban sojin Myanmar  Min Aung Hlaing
Shugaban sojin Myanmar Min Aung Hlaing ©HLA HLA HTAY / AFP
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojin Myanmar da kokarin share al’ummar Musulmin Rohingya.

A cikin makwanni bakwai da suka gabata, ‘yan Rohingya sama da rabin miliyan ne suka tsallaka zuwa Bangladesh saboda tashin hankalin.

Jihar Rakhine ta tsindima cikin tashin hankali ne bayan ‘yan tawayen Rohingya sun kai hari kan ofishin ‘yan sanda a ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.