An tilastawa 'yan gudun hijira komawa Myanmar
Hukumomi a Bangaladesh sun bada sanarwar cewa akwai karin dubban Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a kan iyakar kasar da Myanmar wadanda ke jiran samun damar tsallakowa kasar don samun mafaka, sakamakon kisan gillar da ake ci gaba da yi musu.
Wallafawa ranar:
A cewar hukumomin sun rufe kan iyakokin kasar da 'yan gudun hijirar ke samun tsallakowa, sakamakon yawan da suke ci gaba da yi kowacce rana a kasar.
Ko a makon daya gabata ma, kimanin musulmi ‘yan kabilar Rohingya dubu 10 aka dakatar tsawon kwanaki uku a wani kauye na Anjumanpara kafin ba su izinin shigowa Bangaladesh a ranar Alhamis.
Galibin ‘yan gudun hijirar da ke neman tsallakowa Bangaladesh na kukan rashin abinci a kauyukansu bayan da hukumomi a Rakhine suka hana shigar musu da kayakin Abinci
Wani jami’in tsaro ya ce galibi masunta ne ke tsallako da ‘yan gudun hijirar ta ruwan da ya raba kasashen biyu, lamarin da ya sa aka dakatar da aikinsu na wucin gadi tare da mayar da ‘yan gudun hijira kimanin dubu 15 Myanmar kafin su samu damar tsallakowa ruwan.
Kawo yanzu dai adadin musulmi 'yan kabilar Rohingya da rikici ya tilastawa barin gidajensu ya haura mutum dubu dari shidda a Bnagaladeshi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu