Isa ga babban shafi
Iraqi

Al-Abadi ya kalubalanci Tillerson a kan Iran

Firaministan Iraki Haider Al-Abadi, ya kalubalanci sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da ke cewa har yanzu akwai dimbin dakarun Iran a cikin kasar ta Iraki, inda firaministan ya musanta wannan ikirari.

Firministan Iraqi Haider Al-Abadi
Firministan Iraqi Haider Al-Abadi REUTERS/via Reuters TV
Talla

A lokacin da ya ke ganawa da mahukuntan kasar Saudiyyar ranar lahadin da ta gabata, sakataren wajen na Amurka ya bukaci dakarun Iran da su bar Iraki saboda a cewarsa an kawo karshen yaki da ayyukan ta’addancin da ake yi a kasar, to sai dai a lokacin ganawarsu Tillerson a birnin Bagdaza, Haider Al-abadi ya musanta wannan ikirari.

Al-abadi, ya ce dakarun sa-kai da ake kira Hashed al-Sha’abi wadanda yawansu ya kai dubu 60, dukkaninsu ‘yan kasar Iraki ne ba Iraniyawa a cikinsu, kuma Iraki na tinkaho da su sakamakon rawar da suka taka wajen yaki da ‘yan ta’adda daga shekara ta 2014 zuwa yau.

Amurka dai na zargin cewa yanzu haka akwai daruruwan sojojin Iran da ke ci gaba da kasancewa a cikin kasar ta Iraki, lamarin da Amurka da kawayenta irinsu Saudiyya ke kallo a matsayin shisshigi a lamurran cikin gidin gidan kasar.

Rex Tillerson ya kai ziyarar ba zata ne a birnin Bagadaza a yammacin jiya, bayan da ya kai irin wannan ziyara ta ba zata a kasar Afghanistan inda ya gana da dakarun Amurka da ke kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.