Isa ga babban shafi
Myammar

Babu tabbacin Suu Kyi ta ziyarci kauyukan da aka 'kona

Jagorar siyasa ta kasar Mymamar Aung San Suu Kyi ta kammala ziyarar da ta kai a yankin arewacin jihar Rakhine mai fama da rikici, inda rahotanni ke bayyana cewa ta gana da musulmi ‘yan kabilar Rohingya, wadanda rikicin ya d'aid'aita.

Wannan ne karon farko da Suu Kyi ta kai ziyara jihar Rakhine
Wannan ne karon farko da Suu Kyi ta kai ziyara jihar Rakhine REUTERS/Stringer
Talla

Wannan dai shi ne karo na farko da jagorar siyasar kasar ta Myammar Aung San Suu Kyi ta kai a wannan yanki na arewacin jihar Rakhine tun bayan da ta kama aiki.

Sai dai abinda ba a tabbatar ba shi ne ko jagorar siyasar ta ziyarci daruruwan kauyukan Rohingyawa wadanda ake zargin sojoji sun kona, tare da taimakon mabiya addinin Bhudda na yankin.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun bayyana cewa Suu Kyi ta gana da al’ummar Rohinghya a garin Maungdaw.

Ta kai wannan ziyara ce a kokarin da ta ke yi na nuna wa masu sa ido na cikin gida cewa rikicin ya lafa, ta yadda za a iya fara aikin farfado da yankin.

Suu Kyi dai ta ce ana maraba da ‘yan kabilar ta Rohingya masu son komawa gida, matukar dai sun cika ka’idojin tantancewa na sake shiga kasar.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa dubban daruruwan musulmi yan kabilar Rohingya ne suka tsere daga yankin a sanadiyyar rikicin wanda ya bata sunan kasar ta Myammar a idon duniya.

Majalisar dinkin duniya dai ta bayyana rikicin na Myammar a matsayin wani yunkuri na kawar da wata kabila daga doron kasa.

Sauran kasashe na cigaba da matsa lamba ga gwamnatin kasar da ta samar wa al’ummar ta Rohingya tsaron da ya dace, ta yadda za su samu damar komawa yankin nasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.