Isa ga babban shafi
Iraqi

An gano kabari dauke da gawarwaki 400 a Iraqi

An gano wani kabari dauke da gawarwaki akalla 400 a cikinsa, a wani wuri da ke gaf da birnin Hawija, wanda a baya yake karkashin mayakan kungiyar IS, kafin korarsu daga birnin a watan da ya gabata.

Wani sojan kasar Iraqi yayin nuni ga wani kabari dauke da gawarwaki masu yawa da suka gano a garin Hammam al-Alil bayan kwace shi daga karkashin mayakan IS.
Wani sojan kasar Iraqi yayin nuni ga wani kabari dauke da gawarwaki masu yawa da suka gano a garin Hammam al-Alil bayan kwace shi daga karkashin mayakan IS. REUTERS/Alaa Al-Marjani
Talla

Gwamnan lardin Kirkuk, Rakan Sa’id, ya ce wasu daga cikin mutanen da aka gano, suna sanye ne da kayan fararen hula, yayinda sauran ke sanye da wasu riguna da mayakan IS ke sa wa wadanda suka yankewa hukuncin kisa.

Birnin Hawija mai nisan kilomita 240 daga birnin Bagadaza, ya kasance karkashin kungiyar IS tun a shekarar 2013, kafin sojin Iraqi su ‘yantar da shi a watan da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa, daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu, an gano manyan kaburbura a wurare 72 da ke Iraqi, wadanda a baya suka kasance a karkashin ikon mayakan IS, zalika manyan kaburburan sun kunshi jimillar gawarwaki daga kimanin dubu 5,200 zuwa sama da dubu 15,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.