rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Pakistan Amurka Ta'addanci India

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta gargadi Pakistan bisa sakin Hafiz Sa'id

media
Hafiz Sa'id, yayin tare da magoya bayansa, a lokacin da ya halarci Sallar Juma'a a birnin Lahore. 24 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Mohsin Raza

Amurka ta gargadi gwamnatin Pakistan da cewa, dagantakarsu zata yi tsami, bisa matakin da ta dauka a ranar Laraba, na sakin Hafiz Sa’id, wanda akai wa daurin talala a birnin Lahore, tun a watan Janairu, bisa samunsa da hannu a wani harin ta’addanci da aka kai a kasar India.


Dan haka ne Amurka ta bukaci Pakistan, ta sake kame Hafiz Sa’id domin yi masa hukuncin da ya dace, saboda shirya harin ta’addancin da aka kai a birnin Mumbai na India, wanda ya hallaka, mutane 166, ciki har da Amurkawa.

Sa’id na cigaba da musanta cewa yana da alaka da harin na Mumbai a shekarar 2008, wanda wasu ‘yan bindiga 10 suka bude wuta kan wasu manyan Otal 2, wata cibiyar Yahudawa, da kuma wata tashar jirgin kasa.

Tun a waccan lokacin ne, gwamnatin Amurka ta yi alkawarin bada ladan dala dubu 10, ga duk wanda ya taimaka mata da bayanan da zasu bada nasarar kama Hafiz Sa’id, a kuma yanke masa hukunci.