Isa ga babban shafi

Hamas ta yi watsi da bukatar ta ajiye makamai

Kungiyar Hamas da ke yankin Falasdinu, ta sake yin watsi da bukatar ajiye makamai, yayinda ake tunkarar ranar da aka tsaida, domin ci gaba da tattaunawar sulhu tsakaninta da Isra’ila.

Sojojin rundunar Ezzedine al-Qassam na kungiyar Hamas a zirin Gaza.
Sojojin rundunar Ezzedine al-Qassam na kungiyar Hamas a zirin Gaza. REUTERS/Mohammed Salem/Files
Talla

A maimakon haka Hamas ta yi ikirarin sai ta kai wa Isra’ila jerin hare-hare.

A ranar Juma’a mai ake sa ran kungiyar ta Hamas zata mika ikon kula yankin zirin Gaza zuwa ga, ga gwamnatin Falasdinawa ta Fattah da duniya ta amince da ita.

Tun a shekarar 2007 Hamas ta karbe iko da Gaza, bayan janyewar da Isra’ila a shekarar 2005.

Sai dai kuma bangaren kungiyar Hamas dake dauke da makamai, wato Ezzedine al-Qassam ta sha lawashin ci gaba da kai wa sojojin Isra’ila hare-hare, har sai sun janye da mamayar da suka yi wa yammacin gabar kogin Jordan.

Akalla ‘yan kasar Isra’ila dubu 400 ne ke zaune a yankin yammacin gabar kogin Jordan, tare da Falasdinawa miliyan 3, abinda ya sabawa dokokin kasa da kasa, sakamakon mamaye yankunan akalla Falasdinawan da suka yi ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.