rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lebanon

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hariri ya bayyana janye murabus din da ya yi

media
Firaministan Saad al-Hariri na Lebanon REUTERS/Aziz Taher

Firaministan Lebanon Saad Hariri ya bayyana janye murabus din da ya yi wata guda da ya gabata, bayan wani taron Majalisar ministocin kasar yau talata.


Majalisar ministocin ta bayyana farin cikin ta da matakin, kana kuma ta bayyana matsayin ta na zama ‘yar baruwan mu daga duk wani rikicin da ya shafi kasashen larabawa.

Ana saran Hariri ya ziyarci birnin Paris na Faransa ranar juma’a domin halartar wani taro da za’a yi kan murabus din da ya yi, wanda zai samu halartar Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson.

Murabus din Hariri ya haifar da furgaban barkewar sabon rikicin siyasa da tattalin arziki a kasar da ke fama da rabuwar kawuna.