Isa ga babban shafi
Palestine

Ba mu maraba da zuwan mataimakin shugaban Amurka-Falasdinawa

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ba zai gana da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ba a lokacin ziyarar da Pence din zai kai gabas ta tsakiya cikin watan Disamba.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas.
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Shi ma shugaban kiristoci mabiya darikar Kibdanci na kasar Masar Fafaroma Tawadros II ya soke ganawar da zai yi da Mike Pence din domin nuna adawarsa da matsayar Amurka kan birnin Qudus.

Hakan na zuwa ne bayan matakin da shugaban Amurka Donal Trump ya dauka na tabbatar da Qudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila, matakin da ya janyo sabuwar tarzoma a yankin.

Mai bai wa shugaba Abbas shawara kan harkar diflomasiyya Majdi al-Khaldi ya fadi wa kamfanin dillancin labaru na AFP a ranar Asabar cewa kasar Amurka ta tsallaka duk wasu layuka da aka gindaya, bayan da kasar ta bayyana Qudus a matsayin babban birnin Israila.

Wani lokaci cikin watan Disamba ne ake sa ran Mike Pence zai ziyarci kasar Isra’ila, inda zai ya da zango a garin Bethlehem da ke hannun Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.