rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Falasdinawa Isra'ila Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwamitin tsaro zai fayyace matsayinsa kan Birnin Kudus

media
Dubban 'yan kasar Indonesia a birnin Jakarta, masu zanga-zangar adawa da matakin shugaban Amurka Donald Trump na bayyana Birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila. Reuters/路透社

A wannan Litinin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a domin bayyana matsayinsa dangane da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka, na bayyana Birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra’ila.


Bayanai na nuni da cewa, wannan kuduri zai samun amincewar sauran kasashe mambobi a kwamitin na tsaro.

Sai dai Kafin daftarin ya samu amincewar, tilas ya samu goyon bayan kasashe 9 daga cikin 15 membobi a kwamitin tsaron, ba kuma tare da hawa kujerar naki daga koda kasa guda ba, a tsakanin Amurka, Faransa, China, Rasha, ko kuma Birtaniya, masu kujerun na din din din a kwamitin.

Kasar Masar ce dai ta gabatar da daftarin da ke fatan ganin Kwamitin Tsaron na MDD, ya jaddada birnin Quds a matsayin wanda ke karkashin kulawar Majalisar, abin da ke nufin cewa matakin na Amurka ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Tun a ranar juma’ar da ta gabata ne jami’an diflomasiyyar kasar Masar suka fara tuntubar wakilan sauran kasashe 14 mambobi a kwamitin tsaron, domin neman samun nasarar wannan yunkuri nasu, to amma akwai yiyuwar Amurka za ta iya hawan kujerar na-ki domin hana faruwar hakan.

Sai dai hawan kujerar na-ki a wannan karon mataki ne da zai iya shafar kimar kasar a siyasance.

Kimanin shekara daya da ta gabata, gwamnatin Barack Obama wadda ga al’ada ke bai wa Isra’ila kariya a duk lokacin da aka gabatar da wani kuduri da ya shafi kasar, ta zura ido sauran kasashe a kwamitin tsaron suka jefa kuri’ar da ke neman Isra’ila ta dakatar da gina gidaje a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

To sai dai manazarta na ganin cewa zai kasance abu mai wuya gwamnatin Donald Trump ta dauki irin wannan mataki a wannan karon.