rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Vladimir Putin Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha za ta faɗaɗa sansanin sojin ruwanta da ke Syria

media
Jirgin yakin ruwa na Rasha. REUTERS/Stringer

Majalisar dokokin Rasha ta amince da wata yarjejeniya tsakanin ƙasar da Syria wadda za ta bai wa Rasha ɗin damar bunƙasa sansanin sojin ruwanta da ke a Tartus na Syria.


A ƙarkashin wannan yarjejeniya Rasha za ta samu damar faɗaɗa sansanin, da kuma samar da sabbin kayan aiki ga sojojinta na ruwa.

Hakan na nufin daga yanzu ƙasar za ta iya jibge jiragen ruwa na yaki guda 11, har da masu amfani da makamashin nukiliya.

Tun a watan Janairu ne aka sanya hannu kan yarjejeniyar a ƙasar Syria, inda shugaba Vladimir Purin ya aike da ita ga majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewa.

A wata ziyara da ya kai kwanakin baya, Putin ya bayar da umurnin rage yawan dakarun ƙasar Rasha da ke a Syria, ƙasar da yanzu haka yaƙi ya ɗaiɗaita.