Isa ga babban shafi
Philippines

Philippines: Mutane 200 sun hallaka a ambaliyar ruwa

Jami’an ceto a Philippines suna ci gaba da aikin neman daruruwan mutane ambaliyar ruwa ta rutsa da su a kudancin kasar, sakamakon guguwar da ta afkawa yankin.

Wasu daga cikin daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin Lanao del Norte, na kasar Philippines, Disamba 22, 2017.
Wasu daga cikin daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin Lanao del Norte, na kasar Philippines, Disamba 22, 2017. Aclimah Cabugatan Disumala/via REUTERS
Talla

Sai dai har yanzu jami’an sun gaza kai wa ga wasu sassan na Tsibirin Mindanao inda iftila’in ya fi shafa saboda rashin kyawun yanayi.

Zuwa yanzu mutane 200 jami'an agaji suka tabbatar da cewa sun hallaka, sakamakon zaftarewar kasa da tabo da kuma ambaliyar ruwan da guguwar ta haddasa.

Mutane masu yawan gaske ne suka bace bayan afkawa kudancin kasar da guguwar Tembin ta yi, mai gudun kilomita 80 a sa’a guda, inda ta fi shafar garuruwan Tubod da Piagapo, yayinda kuma ambaliyar ruwan ta shafe kauyen Dalama baki daya.

A halin yanzu guguwar ta tunkari yamacin kasar Vietnam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.