Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Syria sun yi watsi da shirin sulhu a karkashin Rasha

Kungiyoyin ‘yan tawayen Syria sun ce ba za su halarci taron sulhunta rikicin kasar da za a yi cikin watan gobe a Rasha ba.

Wakilan da ke tattaunawar sulhunta rikicin kasar Syria, yayin taro birnin Astana, na kasar Kazakhstan, Disamba 22, 2017.
Wakilan da ke tattaunawar sulhunta rikicin kasar Syria, yayin taro birnin Astana, na kasar Kazakhstan, Disamba 22, 2017. Reuters
Talla

A cewar kungiyoyin, kasar Rasha tana son amfani da damar ce, wajen kauracewa, tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta ke jagoranta a birnin Geneva.

Kungiyoyi 40 ne masu dauke da makamai suka bayyana matsayar da suka cimma, inda suka fito fili suka nun rashin aminta da shiga tsakanin da kasashen Rasha, Turkiya da Iran ke jagoranta ba.

Cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, kungiyoyin sun zargi Rasha da aikata laifukan yaki a sassan kasar ta Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban fararen hula.

Zalika kungiyoyin ‘yan tawayen sun kara da zargin cewa da gangan kasar Rasha taki matsawa gwamnatin Bashar Al-Assad lamba domin gaggauta cimma yarjejeniya da su da zata kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Ranakun 29 da kuma 30 na watan Janairun shekara mai kamawa, kasashen Rasha, Turkiya da Iran suka tsaida domin sake jagorantar tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Syria da ‘yan tawayen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.