Isa ga babban shafi
Iran

Ba za mu lamunci tayar da hankali ba-Rouhani

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce dole ne gwamnati ta bayar da kafar yin suka daga ɓangarori daban-daban, sai dai ya ce ba za a lamunci tayar da rikici ba.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani. ©REUTERS/Stephanie Keith
Talla

Wannan ne karo na farko da Rouhani ya yi jawabi bayan ɓallewar zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin ƙasar da aka kwashe yini uku ana yi.

Kafar yaɗa labaru ta Iran ta ruwaito shugaban a lokacin taron majalisar ƙasar, yana cewa neman kawo gyara ya sha banban da tayar da hargitsi ko kuma ɓarnata kayan gwamnati.

Kuma a gefe guda shugaban na Iran ya soki shugaban Amurka Donald Trump game da martaninsa kan abinda ke faruwa a kasar, inda ya ce Trump din makiyin Iraniyawa ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.