rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Amurka Donald Trump Korea ta Kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Makunnin Nukiliya na kan teburina-Kim Jong-Un

media
Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-Un Reuters/路透社

Shugaban Kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce shifa makunnin Nukiliya na kan teburinsa don haka Amurka ta shiga taitayinta.


Shugaban ya yi wannan barzanar ce a sakonsa na Sabuwar shekara, inda ya ce a shirye ya ke ya tatttauna da koriya ta kudu, har ya ma tura tawagar ‘yan wasan kasar Olympic.

Kim Jong-Un ya ce ya zama dole su ci gaba da kera makaman nukiliya da mai linzami tare da jadada cewa kasarsa ta cim-ma burinta kuma za ta ci gaba da fadada shirin domin kariyar ce agareta.

Koriya dai ta jima tana nanata cewa tana bukatan makamin nukiliyar ne domin kare kanta daga Amurka, ta na kuma ci gaba da kokarin inganta shirinata da zai iya tarwatsa Amurkan.

Shugaba Trump na Amurka ya mayar da kakausar martani kan kowanni kwajin da kasar ta yi, inda ya yi barazanar ruguza Pyongyang da shi kansa Kim da ya bayyana a matsayin wanda ya shirya kisa.

Sai dai a maimakon hakan ya tsoratar ko karya lagon Koriya duk da takukuman da ake kakabata, Kim na sake gaban kansa da aike sakonin barzanar ga Amurka.