rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Amurka Majalisar Dinkin Duniya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta zargi makiyanta da haddasa boren 'yan kasar

media
Shugaban Juyin Juya Halin Musulunci na kasar Iran Ali Khamenei. AFP

Jagoran juin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamene'i ya zargi kasashen turai da rura wutar boren da ‘yan kasar suka shafe kwanaki suna yi.


Zuwa yanzu sama da mutane 20 ne suka hallaka a wannan zanga-zanga, da ‘yan kasar ke ci gaba da yi, dangane da koma bayan tattalin arziki.

Tuni dai kasar Amurka ta yi watsi da wannan zargi tare da neman nemi kwamitin tsaro da hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya su taron gaggawa kan zanga-zangar kasar ta Iran da ke neman rikidewa zuwa rikici.

Cikin jawabinsa na farko kan rikicin jagoran juyin juya halin Musuluncin Iran, ya ce makiyan kasar ne suka shirya makirci ya hanyoyin da suka hada da amfani da kudi, makamai, siyasa da kuma bayanan sirri wajen samun nasarar tayar da kazamin bore a kasar.

A daren Litinin kadai akalla mutane 8 suka hallaka, kidayar da ta kara yawan rasa rayukan da aka yi zuwa mutane 22, tun bayan fara wannan zanga zanga a ranar 28 ga watan Disambar bara a garin Mashhad.

‘yan kasar sun soma wannan zanga-zanga ce domin nuna bacin ransu kan tashin farashin kayan masarufi da kuma karuwar rashin ayyukan yi da akalla kashi 28, kafin daga bisani ta fadada zuwa tsantsar adawa da gwamnati.