rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Iran ta yi shelar kawo karshen boren 'yan kasar

media
Dubban 'yan kasar Iran, yayin da suke gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan gwamnati. 3 Janairu, 2018. REUTERS

Dubban al’ummar kasar Iran, sun fara zanga-zangar nuna goyon bayan gwamnati, bayan shafe kwanaki shida wasu dubban ‘yan kasar suna gudanar zanga-zangar adawa, wadda ta tasamma rikidewa zuwa kazamin bore.


Zanga-zangar goyon bayan gwamnatin da aka fara a jiya Laraba ta zo ne kafin babban hafsan sojin Juyin juya halin Iran Mohammed Ali Ja’afari ya yi shelar kawo karshen boren da ake yi wa gwamnati.

Ja’afari ya sha alwashin hukunta wadanda suka haddasa boren, wadanda ya ce, sun sami horo na musamman wajen tada rikici.

Akalla masu zanga-zangar adawa da gwamnati 530 jami’an tsaron Iran suka kame, 450 a babban birnin kasar Teheran, yayinda aka kame 80 a birnin Arak.

Zanga-zangar da ta faro domin nuna bacin rai kan koma bayan tattalin arziki da rashin aikin yi, sai da ta bazu zuwa biranen kasar 10 cikin harda Teheran.