rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Iran Diflomasiya Nukiliya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta kakabawa kamfanonin Iran biyar takunkumai

media
Shugaban kasar Amurka Donald Trump. REUTERS/Jim Bourg/File Photo

Amurka ta sanya takunkumi kan wasu kamfanonin Iran guda biyar, bayan ta zarge su da yin aiki tare da gwamnatin kasar wajen mallakar haramtaccen makami mai linzami.


A karkashin sabbin takunkuman, za a kwace dukkanin kadarorin kafanonin guda biyar da suke yankunan da ke karkashin Amurka, zalika haramun ne duk wani ba Amurke ya gudanar da wata huldar kasuwanci tsakaninsa da kamfanonin.

Sakataren baitil malin Amurka, Steven Mnuchin ya alakanta daukar mataki da zanga-zangar da aka gudanar a Iran, in da ya ce, ya kamata kasar ta mayar da hankali kan inganta rayuwar al’umma a maimakon kashe kudade kan haramtaccen makami mai linzami.

Mnuchin ya kara da cewa, gwamnatin Amurka zata ci gaba da kalubalantar kokarin Iran na aikata ba daidai ba, ta hanyar daukar sabbin matakai na kakaba mata Karin takunkumai don ladabtar da ita bisa aikata laifukan take hakkin dan adam.