rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Kudu Korea ta Arewa Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Korea ta arewa da ta Kudu sun tsaida ranar tattaunawar sulhu

media
Amincewa da tattaunawar sulhun tsakanin kasashen biyu bayan rikici tsawon shekaru ta biyo bayan kalaman da shugaba Kim Jung-Un ya fitar na bude kofar tattaunawa da duk wata kasa da ke bukatar hakan. 路透社

A karon farko cikin fiye da shekaru biyu, Kasashen Korea ta Arewa da Korea ta Kudu, sun amince su fara tattaunawar sulhu a ranar Talata mai zuwa. An shirya tattaunawar za ta gudana, a kauyen Panmunjom, da ke kan iyakar kasashen biyu, don kawo karshen tsamin dangantaka tsakani.


Tun a ranar Larabar da ta gabata Gwamnatin Korea ta Arewa ta mayar da layin waya tsakaninta da Korea ta Kudu, a lokacin da dagantakarsu ta kara yin tsami a dalilin shirin mallakar karfin makaman Nukiliyar da Korea ta Arewa ta karfafa.

Tun daga watan Yunin shekarar 1950 yakin da yayi sanadin mutuwar sama da mutane miliyan biyu ya barke tsakanin Korea ta Arewa mai samun goyon bayan tarayyar Soviet da kasar China da kuma Korea ta Kudu, wadda dakarun Amurka da na Majalisar dinkin duniya ke marawa baya.

Babban dalilin barkewar yakin bangarorin biyu daya tilasta kai wa ga rabasu zuwa kasashe biyu bayan kasancewarsu a dunkule a baya, shi ne adawa da tsarin mulkin Kwaminisanci da bangaren Korea ta Kudu mai goyon bayan Amurka ke yi, sabanin dabbaka tsarin da Korea ta Arewa mai goyon bayan tarayyar tarayyar Soviet .