rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Amurka Nukiliya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Amurka na gaf da janyewa daga yarjejeniyar Nukiliyar Iran"

media
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani a lokacin da yake ganawa da 'yan majalisar dokokin kasar a birnin Teheran, bayan kawo karshen boren adawa da gwamnati da wasu 'yan kasar suka tayar. 1, Janairu, 2017. HO / IRANIAN PRESIDENCY / AFP

Gwamnatin Iran, ta gargadi kasashen duniya da su shiryawa yiwuwar janyewar Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma, tsakaninta da manyan kasashen turai, dangane da shirinta mai tattare da shakku na inganta makamashin nukiliya.


A shekarar 2015 Iran ta cimma yarjejeniyar tsakaninta da manyan kasashen turai da kuma shugabancin EU, wadda a karkashinta kasar ta Iran ta amince da jingine shirinta na cigaba da inganta makamashin na Nukiliya, wanda zai bata damar mallakar makaminsa. A madadin haka ne, kasashen suka amince da dage takunkuman karya tattalin arzikin da suka kakaba mata a baya dangane da shirin nata.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya dade yana adawa da yarjejeniyar, wadda ta kasance mai muhimmanci da Amurka ta cimma a zamanin mulkin Barrack Obama, ta fuskar manufofin kasashen ketare.

Yayinda ya ke mai da martani kan yiwuwar janyewar Amurka daga yarjejeniyar, kakakin ma’aikatar wajen Iran Bahram Ghasemi, ya ce muddin hakan ta tabbata, Iran zata dauki kwakkwaran mataki na raddi.

A karshen makon nan Ministan harkokin wajen na Iran, Muhd Javad Zarif zai yi tattaki don ganawa da wakilan kasashen Birtaniya, France, Jamus, da kuma na kungiyar tarayyar turai EU, sai dai ya musanta cewa tattaunawar zata mayar da hankali ne kan boren da ‘yan kasar suka yi a baya-bayan nan da yayi sanadin mutuwar mutane 21.