rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amnesty Hakkin Dan Adam Myanmar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amnesty ta bukaci tsananta bincike kan kisan 'yan Rohingya

media
A baya-bayan nan ne dakarun Sojin Myanmar suka amince da kisan 10 cikin dubban musulmai 'yan kabilar Rohingya da aka shafe tsawon watanni ana musu kisan gilla tare da kone dukiyoyinsu. REUTERS/Hannah McKay

Daraktan da ke kula yankin kudu-maso-gabashin Asia na kungiyar Amnesty International ya bukaci a gudanar da bincike don tabbatar da zarge-zargen kisan kiyashi da kuma azabtar da yan kabilar Rohingya, bayan da sojin kasar suka amince da cewa suna da hannu wurin kashe wasu daga cikin yan kabilar.


James Gomez ya fadi haka ne bayan da dakarun na Myanmar suka fitar da wata sanarwa kan kashe muntane 10 na kabilar ta Rohingya.

Darakatan yankin na kungiyar Amnesty ya ce da alama wannan bayani da ya fito soman-tabi ne a kan irin abubuwan da za a iya bankadowa.

Ya kara da cewa wannan ya kawo karshen musawar da hukumomin kasar ke yi na cewa ba su da hannu ko kadan a cikin kashe-kashen na yan kabilar Rohingya.

A jiya ne dai babban hafsan sojin kasar Myanmar ya ce jami’an tsaron kasar na cikin wadanda suka aikata kisan yan kabilar Rohingya guda 10 a cikin watan satumbar bara.

Sanarwar ce karo na farko da jami’an tsaron kasar suka amince cewa suna da hannu a cikin kashe-kashen muslmai yan kabilar Rohingya na kasar, wanda ya haifar da ficewar mutanen daga kasar.

A cikin bayanin da ofishin hafsan hafsoshin sojin na Myanmar ya fitar, ya nuna cewa sojoji ne suka kama mutanen guda 10, inda daga baya suka yanke shawarar kashe su a kauyen Inn Dinn.

Kafin wannan lokaci dai dakarun Myanmar sun musa aikata wani laifi game da kisan na yan kabilar Rohingya.

Sai dai a wani mataki da ake ganin na kokarin wanke kansu ne da yammacin ranar Laraba sojojin suka fitar da wata sanarwa inda suka ce lokacin da kisar ta faru ba a sanar da manyan jami’an soji ba.