Isa ga babban shafi
Myanmar

Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya na cikin hadari

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa nan da watanni kalilan halin kuncin da ‘yan kabilar Rohingya ke ciki a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bangladesh zai kara tsananta, matukar ba a fara aikin mayar da su Myanmar ba.

A baya-bayan nan ne 'yan gudun hijirar Rohingya suka gindaya sharudda ga hukumomin kasar dangane da batun komawarsu gida.
A baya-bayan nan ne 'yan gudun hijirar Rohingya suka gindaya sharudda ga hukumomin kasar dangane da batun komawarsu gida. AFP
Talla

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman da gwamnatin Myanmar ta haramtawa shiga kasar Yanghee Lee, ta ce akwai yiwuwar zabtarewar kasa a sansanin ‘yan gudun hijira na Cox’s Bazar lamarin kuma da zai iya shafar daruruwan ‘Yan kabilar ta Rohingya la’akari da galibinsu suna sansanin.

A watan nan ne dai jakadun majalisar dinkin duniya za su isa kasar ta Myanmar don gudanar da bincike kan zargin cin zarafin bil’adaman da aka yiwa musulmi ‘yan kabilar Rohingya, da ya tilasta musu ficewa daga kasar don tsira da rayukansu.

Jami’an majalisar za kuma su tattauna kan batun Fyade da kisan gillar da ake zargin jami’an tsaron kasar da aikatawa, wanda majalisar ta bayyana a matsayin yunkurin shafe wata kabila.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta yi magana kan sharuddan da ‘yan Rohingyar suka gindaya dangane da batun komawarsu gida, duk da cewa yawan Musulmi 'yan Rohingyar da ke gudun hijira a kasashen waje ya tasamma miliyan guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.