rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

India

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Arrangama tsakanin mabiya addinin Hindu da jami’an tsaro a India

media
Arrangama tsakanin mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra’ayi da jami’an tsaro REUTERS/Amit Dave/File photo

An samu arrangama tsakanin mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra’ayi da jami’an tsaro a arewacin kasar India, bayanda fusatattun masu zanga-zangar suka yi barazanar kai wa gidajen Cinema hare-hare a sassan kasar, idan suka haska Fim din Padmavati da kotun kolin kasar ta bada umarnin saki.


Mabiya addinin Hindun na kallon Fim din a matsayin cin zarafi a garesu bisa yadda aka nuna soyayya tsakanin wata sarauniyar Hindu da wani Muslmi basarake.

‘Yan Sanda da sauran jamian tsaro sun karfafa tsaro a gidajen sinima tun ajiya saboda fargaban kazamin bore.