rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Taliban Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yawan wadanda harin bam ya hallaka a Kabul ya kai 95

media
Shingen jami'an 'yan sanda da kungiyar taliban ta kai harin a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan. Janairu 27, 2018. REUTERS/Omar Sobhani

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bam da aka boye a cikin wata motar daukar marasa lafiya, da zuwa yanzu jami’an agaji a Afghanistan suka ce yawan wadanda suka hallaka a dalilinsa, ya kai akalla mutane 95, yayin da yawan wadanda suka jikkata ya kai 158.


An kai harin ne a yau Asabar a gaf da wani shingen bincike na ‘yan sandan kasar da ke kusa da ofisoshin jakadancin kasashen ketare da suka hada da na Sweden, Kungiyar tarayyar turai, da kuma India, a babban birnin kasar Kabul.

Karo na biyu kenan da Taliban ke ikirarin kai hari a birnin Kabul, bayan wanda ta kai makon da ya gabata kan wani Otal, inda suka hallaka mutane 20.

A farkon makon nan ne kuma kungiyar IS ta kai hari kan ofishin bada agaji na 'Save the Children' a birnin Jalalabad, inda ta hallaka mutane 3.