rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rayuka sun salwanta yayin rikici tsakanin ƴan-bindiga a Yemen

media
Garin Aden na kudancin Yemen. STRINGER / AFP

Rahotanni daga birninn Aden da ke yammacin ƙasar Yemen sun tabbatar da cewa mutane da dama sun rasa rayukansu wasu kuma sun samu raunuka lokacin da aka yi artabu tsakanin ƙungiyoyin ƴan-bindiga.


Mazauna birnin sun ce ƙungiyoyin ƴan-bindiga biyu da ke da mabiya watse a unguwanni daban-daban ne suka yi musayar wuta tsakanin su a ranar Lahadi.

Wannan rikici ya zo ne bayan ƙarewar wa'adin da ƴan adawa suka bai wa gwamnatin ƙasar na ajiye mulki a ranar Lahadi.

Gwamnatin dai na iko ne da kimanin kashi 4 cikin 5 na ƙasar, sai dai yan tawaye a Aden na yunƙurin farfado da zancen cin-gashin-kai na yammacin ƙasar.