rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya buƙaci duniya ta yaƙi Taliban

media
Shugaban kasar Amurka Donald Trump. REUTERS/Yuri Gripas

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce harin da Taliban ta kai a Kabul, babban birnin Afghanistan ya ƙara zaburar da Amurka da kuma ƙawayenta na Afghanistan a ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da ƙungiyar.


Ya kuma ce ya zama wajibi dukkanin ƙasashen duniya su haɗu wajen murƙushe ƙungiyar wadda ta ɗauki alhakin kai mummunar harin da ya yi sanadiyyar rayukan mutanen kusan 100.

Lokacin da ya yi tsokaci kan al’amari sakataren harkokin waje na Amurka Rex Tillerson ya ce harin na ranar Asabar ya karya ƙa’idoji na ƙasashen duniya.

An kai harin ne dai ta amfani da motar daukan marasa lafiya.