rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Qatar Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Goyan bayan Amurka zuwa Qatar a yaki da ta'addanci

media
Cheikh Tamim ben Hamad al-Thani, Sarkin Qatar REUTERS/Naseem Zeitoon

Kasar Amurka ta yaba da rawar da Qatar ke takawa wajen yaki da ta’addanci, inda tayi gargadin cewar rikicin da take yi da Saudi Arabia da kawayen ta na haifar da tarnaki wajen yakin.


Sakataren harkokin waje Amurka Rex Tillerson tare da takwaran sa na tsaro Jim Mattis na ci gaba da tattaunawa domin ganin an magance rikicin dake tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu haka barakar da aka samu tsakanin Qatar da kasashen dake tekun fasha a karkashin Saudi Arabia ya kama hanyar cika watanni 8 kenan ba tare da bangarorin biyu sun amince su gana gaba da gaba ba.