rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Syria Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kakkaɓo jirgin yaƙin Rasha

media
Jiragen yakin soji. REUTERS/US Navy/

Matuƙin jirgin yaƙi na Rasha guda ɗaya ne aka kashe bayan da aka kaɓo jirgin da yake ciki sa’ilin gumurzu a yankin Idlib na Syria.


Tun farko dai ƴan-twayen Syria sun bayar da sanarwar kabo jirgin.

Rasha ta ce an kabo jirgin ne da wani makami wanda aka harba daga doron ƙasa a wani yanki da ke ƙarƙashin ƴan-tawayen Al Nusra.

Sanarwar da ma’aikatar tsaron ƙasar Rasha din ta bayar ta ce Rasha da Turkiyya na ƙoƙarin ganin sun ƙwato gawar matuƙin jirgin.