rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Majalisar Dinkin Duniya Myanmar Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

MDD ta zargi Korewa ta Arewa da fasakaurin makamai

media
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un. Reuters/路透社

Jami’an sa ido na Majalisar Dinkin Duniya sun ce, Korea ta Arewa ta bijirewa takunkuman da Majalisar ta kakaba mata, na haramcin fitar da wasu kayayyaki zuwa ketare.


Rahoton ya ce bijirewa takunkuman ya bai wa kasar damar samun kudaden shiga akalla dala miliyan 200 a shekarar 2017.

Jami’an sun ce Korea ta Arewa ta samu makudan kudaden shigar ne daga cinikayyar makamashin Kwal da ta fitar zuwa Rasha, China, Korea ta Kudu, Malaysia da kuma Vietnam, inda ta yi amfani da takardun da ke nuna kwal din ya fito ne daga kasashen Rasha da China.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar, ya kuma zargi Korewa ta Arewa, da fasa kaurin makamai zuwa kasashen Syria da kuma Myanmar.