rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Kudu Olympic Korea ta Arewa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zanga-zanga ta barke gabanin gasar Olympics ta bana

media
Wasu daga cikin mambobin Korea ta Arewa da za su fafata a gasar Olympics a Korea ta Kudu AFP

Gabanin bude gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta sanyin hunturu a Korea ta Kudu,  zanga-zanga ta barke a manyan titunan birnin Gang Neung da zai karbi bakwancin gasar. Masu zanga-zangar dai na rera wakokin cin zarafin shugaban Korea ta Arewa  Kim Jong-un tare da daga hotunansa cikin siffar wani katon naman daji da ake kira da gwanki.


Cikin yanayin fushi, daruruwan masu zanga-zangar ke rera wakokin la’antar gasar tare da cewa ba sa kaunar wannan gasar tun da an fifita makiyansu akansu.

Tun a kwanakin baya ne jama’ar kasar ke ta mahawara kan yadda aka yi aka bai wa makwabciyarsu, Korea ta Arewa damar shiga gasar, in da jama’ar ke nuna fargabarsu game da abin da ka iya biyo baya, wasu kuma ke farbaga kan cewa, shugaba Kim Jong-Un ka iya samun damar aika 'yan leken asiri cikin kasar.

'Yan wasa 140 ne suka iso Korea ta Kudun daga Arewacin kuma sun samu kyakyawar tarba, abin da ya kara bakanta ran wasu 'yan kasar.

Park Seyung guda ne daga cikin 'yan zanga-zangar da ya yi tattaki daga birnin Seoul ya ce, "ba su ga amfanin gasar ba kuma a fakaice kawai manufofin shugaban Korea Kim Jong-Un za a aiwatar, amman idan ba don haka ba ta yaya za’a baiwa makiya damar zuwa cikin kasarmu"

Daga bangaren Korea ta Arewan dai, sun aike da daruruwan dakaru zuwa yankin kudancin don yi wa 'yan wasan rakiya, kuma daga cikin su har da 'yar uwar shugaban kasar.

A karon farko dai za daga tutocin kasashen biyu ne wuri guda masu launin shudi da fari, lokacin haduwarsu a wasan da za su yi tare.