rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Kudu Korea ta Arewa Wasanni Olympic

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An fara wasannin Olympics da kasashe 92

media
An tanadi kusan nau'ikan wasanni dubu 3 don kawata gasar ta Olympics wadda ke samun halartar kusan kasashen duniya dari ciki har da 8 daga Nahiyar Afrika. REUTERS/Toby Melville TPX IMAGES OF THE DAY

An fara gudanar da wasannin Olympics da Korea ta kudu ke karbar bakoncinta, bayan da aka gudanar da bikin bude filin wasan a safiyar inda akalla kasashe 92 suka fito don nuna tawagarsu ga idon duniya.


Ana ganin dai wasannin Olympics din a bana za su fi kayatarwa fiye da wadanda suka gabata ganin yadda wannan karon aka tanadi kala-kalar wasanni har guda dubu 3.

Daga nahiyar Afrika kasashen da za su halarci gasar sun hada da Afrika ta kudu da Ghana da Najeriya da Kenya da Madagascar da Marocco da Togo da kuma Eritrea.

Wani abin kayartawa ga bikin bude gasar wasannin Olympics din shi ne yadda kasashen Korea ta kudu da Korea ta arewa suka fito a karkashin tuta guda wato asalin tutar Korea.