rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Philippines ICC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun ICC ta kaddamar da bincike kan shirin shugaban kasar Philippines

media
Rodrigo Duterte Shugaban kasar Philippine REUTERS/Romeo Ranoco

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, ICC ta kaddamar da bincike kan shirin shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte na yaki da tu’ammuli da miyagun kwayoyi da ya kaddamar a watan Yuly na shekarar 2016, wanda cikinsa aka hallaka dubban ‘yan kasar.


Babbar mai gabatar da kara a kotun ta ICC Fatou Bensouda, ta ce binciken zai mayar da hankali ne kan zargin Duterte da take hakkin dan adam.

Akalla ‘yan kasar Philippines dubu 4,000, ‘yan sandan kasar suka hallaka, bisa da’awar sun same su da laifin tu’ammuli da miyagun kwayoyi ko kuma safararsu.