rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Syria Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabon rikici tsakanin Iran da Isra'ila

media
Hassan Rohani Shugaban kasar Iran Handout / Iranian Presidency / AFP

A yau asabar kasar Iran ta zargi Isra’ila da shirya makarkashiya da kage bayan da hukumar tsaron Isra’ila ta bayana kakabo wani jirgi marasa matuki na kasar Iran.


Mai magana da yahu ministan harakokin wajen Iran Bahram Ghassemi ya bayana Isra’ila a matsayin wacce ke kokarin yi rufa –rufa ga kisan da take aikatawa a yankunan Syria da gabas ta taskiya.

A matakin mayar da martani daga Syria bayan da Isara’ila ta aike da jiragen ta na yaki zuwa wasu yankunan kasar Syria, rundunar tsaron Syria ta yi nasarar kakabo daya daga cikin jiragen yakin Isra’ila wanda aka bayyana cewa matuki ya samu munanan raunuka.

Jami’in Diflomasiya na Iran ya karasa da cewa kasar sa ba ta aike da soji ba a Syria, sai dai ta na dafawa dakarun Syria da shawarwari da dabaru na yaki.