rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila Iran Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jiragen yakin Isra'ila sun sake kai farmaki cikin Syria

media
Wani sashi na arewacin kasar Syria, inda jirgin yakin Isra'ila ya fadi bayan harbo shi kasa da soji masu biyayya ga Iran da Syria, suka yi. AFP / Jack GUEZ

Fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gargadi Iran da cewa, Isra’ila zata maida martani ta fuskar karfin soji, kan duk wata barazanar tsaro daga gareta.


Gargadin na Isra’ila ya zo ne bayan kai farmaki na biyu da jiragen yakinta suka yi kan wasu cibiyoyin tsaro 12 a Syria wadanda ke karkashin Iran da kuma gwamnatin Syria.

Isra’ila ta ce ta kai farmakin ne bayan da ta kakkabo wani jirgin leken asiri na Iran da ke kokarn shiga cikin kasar daga Syria.

Netanyahu ya jaddada cewa Isra’ila zata kalubalanci duk wani yunkuri na Iran wajen kafa cibiyoyin sojinta a Syria, abinda ta ke kallo a matsayin babbar barazana gareta.