rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Kudu Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Korea ta Kudu ta yi wa Choi daurin shekaru 20

media
Choi Soon-sil ta kasance dadaddiyar aminiyar tsohuwar shugabar kasar, Park Guen-hye Yonhap via REUTERS

Wata Kotun Korea ta Kudu ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 kan Choi Soon-sil, aminiyar tsohuwar shugabar kasar, Park Geun-hye saboda samun ta da hannu a wata badakalar cin hanci da rashawa da ta yi sanadiyar tsige Guen-hye daga kujerarta. Kotun da ke birnin Seoul, ta kuma ci tarar Choi sama da dala miliyan 16.


Choi Soon-sil ta kasance babbar jigon da aka zarga da hannu dumu-dumu a badalakar rashawar da ta yi sanadiyar tsige Park Guen-hye da ta kasance mace ta farko da ta shugabancin kasar.

Choi ta shafe tsawon shekaru 10 a matsayin babbar mai bada shawara ga uwargida Park wadda ita ma ke fuskantar tuhumar kan laifin rashawar duk da dai ta musanta aikata ba dai dai ba.

An zargi Choi da yin amfani da kusancin da ke tsakaninta da tsohuwar shugabar wajen matsin lamba ga wasu kamfanoni da suka hada da Samsung har ta karbi sama da dala miliyan 13 daga hannunsu da sunan agazawa gidauniyar da ta ke jagoranta.

Alkalin kotun ya ce, laifin da Choi ta aikata na da matukar girma, in da ya ce ta yi amfani da matsayinta wajen karbar cin hanci, sannan kuma ta wuce makadi da rawa wajen katsalandar a sha’anin tafiyar da gwamnatin kasar.

Gabanin hukuncin na yau, Choi na zaman gidan kaso na shekaru 3 saboda wani laifi daban na nema wa ‘yarta alfarma, yayin da aminiyarta, Guen-hye ke ci gaba da tsare kafin yanke ma ta hukunci a cikin wanna shekara.