Isa ga babban shafi
Syria

Gwamnatin Syria ta sake musanta amfani da makami mai guba

Gwamnatin Syria ta musanta mallakar makamai masu guba, tare da yin alla wadai da duk wanda ke amfani da makaman.

Wata mata da ake kokarin bai wa agajin gaggawa, bayan da ta jikkata sakamakon farmakin jiragen yaki kan kauyen Douma da ke gabashin yankin Ghouta a Syria.
Wata mata da ake kokarin bai wa agajin gaggawa, bayan da ta jikkata sakamakon farmakin jiragen yaki kan kauyen Douma da ke gabashin yankin Ghouta a Syria. REUTERS/ Bassam Khabieh
Talla

Kalaman na Syria, sun biyo bayan gargadin da kasar Faransa ta yi gwamnatin Bashar al Assad na kaddamar da farmaki kan dakarunsa, muddin bincike ya tabbatar da cewa, sun yi amfani da makamai masu guba wajen kai wa yankunan ‘yan tawaye hare-hare.

Yanzu haka dai ayarin farko na motocin agaji sun isa yankunan kasar Syria, da ke da sarkakiyar gaske, wadanda a baya dakarun gwamnatin suka mamaye.

Jami’an agajin sun fara isa yankin gabashin Ghouta, inda a makon da ya gabata sama da fararen hula 220 suka hallaka, sakamakon farmakin jiragen yakin Rasha da Syria kan ‘yan tawaye, duk da cewa yankin na daga cikin yankunan kasar Syria da aka haramta kai farmaki kansa har zuwa wani lokaci.

A ranar Talata da ta gabata, shugaban Faransa Macron zai bada umarnin kaddamar da farmaki kan sojin Syria, muddin ta bayyana gwamnatin ta yi amfani da makamai masu guba da aka haramta amfani dasu kan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.