Isa ga babban shafi
China

China ta gargadi Amurka kan kakabawa Korea ta Arewa takunkumai

China ta Bukaci Amurka ta janye sabbin takunkunmai masu tsauri da ta kakabawa kasar Korea ta Arewa, inda ta ce aiwatar da takunkunman ka iya kawo nakasu ga kyakkyawar Diflomasiyya da ke tsakaninsu.

Shugaban kasar China Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump
Shugaban kasar China Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria/File Photo
Talla

Bukatar da China ta biyo bayan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, na sanyawa akalla kamfanoni 28 da kuma wasu jiragen ruwa 27 takunkumai na hana safara ko fasa kaurin makamashin kwal da man fetur na Korea ta Arewa.

Zalika Trump ya haramtawa Amurka kulla duk wata hulda tsakaninsu da kamfanonin da ke ayyukansu a kasashen Korea ta Arewa, China, Taiwan da kuma Hong Kong.

Shugaban Amurkan ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake kakaba wasu sabbin takunkuman masu tsauri a nan gaba, idan har wadanda aka kakabawa Korea ta Arewan a baya bayan nan basu yi tasirin da ake bukata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.