rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen Saudiya Iran ISIL

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan kunar bakin wake sun hallaka mutane 14 a Yemen

media
Mayakan IS suna ci gaba da kai munanan hare-hare a Yemen. Reuters

Akalla mutane 14 suka hallaka yayin da wasu 40 suka jikkata, a lokacin da wasu ‘yan kunar bakin wake tare da ‘yan bindiga suka yi yunkurin kutsa kai cikin Headikwatar yaki da ta’addanci da ke birnin Aden na kasar Yemen.


Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin, wanda jami’an tsaro suka ce ‘yan kunar bakin wajen sun tarwatsa bama-baman da suka cika wasu motoci biyu da su, yayin da wasu ‘yan bindiga 6 sukai yunkurin kutsa kai ta karfin tsiya cikin Hedikwatar.

Sai dai yunkurin na su bai yi nasara ba, kasancewar jami’an tsaro sun hallaka baki dayan maharani.

Karo na farko kenan da irin wannan harin ya auku a birnin na Aden, tun bayan musayar wutar da aka yi tsakanin ‘yan tawayen Houthi da jami’an tsaron gwamnatin shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi, dangane da kokarin karbe cikakken iko da birnin.

Gwamnatin Hadi da mai samun goyon bayan Saudiya, ta ayyana birnin na Aden a matsayin hedikwatarta.

Tun a shekarar 2015 ake tafka kazamin yaki tsakanin mayakan na Houthi masu samun tallafin Iran da kuma gwamnatin Abd-Rabbu Mansour Hadi da Saudiya ke marawa baya.