Isa ga babban shafi
Syria

Fararen hula sun ki ficewa daga yankin gabashin Ghouta

Fararen hular dake zama a yankin gabashin Ghouta da ke Syria, sun ki amincewa da tayin Rasha na ficewa daga yankin, yayin da aka shiga rana ta uku da shirin tsagaita wutar da Moscow ta sanar.

Wani sojan gwamnatin Syria tsaye a filin da aka girke motocin daukar marasa lafiya,  yayin da ake dakon fitowar fararen hula.
Wani sojan gwamnatin Syria tsaye a filin da aka girke motocin daukar marasa lafiya, yayin da ake dakon fitowar fararen hula. Yahoo
Talla

Rahotanni sun tabbatar da cewa babu ko da mutum daya daga cikin mazauna yankin akalla 400,000 da ya yi kokarin shiga manyan motocin Safa da rasha ta samar domin kwashe fararen hula.

Tun bayan amincewa da kudurin tsagaita wuta a yakin na Syria da kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi, akwai akalla motocin dauke da kayan abinci da kuma magunguna, da ke dakon samun kai agaji ga fararen hular da yaki a rutsa da su a yankin gabashin na Ghouta.

Hare-haren da jiragen yaki suka kwashe kwanaki 10 suna kai wa yankin na gabashin Ghouta, ya hallaka mutane sama da 600.

Majalisar Dinkin Duniya na cigaba da kira ga bangarori biyu da ke rikicin, su tsagaita wuta kamar yadda aka shirya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.