Iran ta bukaci kasashen turai su lalata makaman nukiliyarsu
Kasar Iran ta ce, ba zata tattaunawa da kasashen turai da Amurka ba, kan shirinta na ci gaba da kera manyan makamai masu Linzami, sai dukkanin kasashen, sun lalata makaman nukiliyar da suka mallaka da sauran makamai masu linzami da ke cin dogon zango.
Wallafawa ranar:
Iran ta jaddada cewa munafar shirinta na kera manyan makamai masu linzami ya dogara ne akan samar wa da kanta tsaro daga duk wata barazana, kuma shirin kera makamai masu linzamin ba shi da alaka da yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a 2015.
Iran ta amince da dakatar da shirinta na inganta makamashin nukilya wanda ta musanta cewa kokarin kera makami mai Linzami, sai dai Iran din taki amincewa da bukatar zama a tattauna da ita kan shirin ta kan mallakar karin manyan makamai masu linzami.
Tuni dai kasashen turai suka fara tattaunawa kan rawar da Iran ke takawa a yankin gabas ta tsakiya, kuma a cikin wannan wata na Maris zasu gudanar da makamancin taron akan Iran, a kasar Italiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu