Isa ga babban shafi
Syria

Turkiya ta kammala kwace Afrin daga hannun Kurdawa

Rundunar sojin Turkiya ta sanar samun nasarar karbe iko da ilahirin yankin Afrin da ke arewacin Syria, tare da taimakon ‘yan tawayen kasar da ke mara musu baya.

Wasu mayakan 'yan tawayen Syria da ke marawa sojin Turkiya baya, yayinda suke murnar kwace iko da yankin Afrin.
Wasu mayakan 'yan tawayen Syria da ke marawa sojin Turkiya baya, yayinda suke murnar kwace iko da yankin Afrin. REUTERS/ Khalil Ashawi
Talla

Turkiya ta samu wannan nasarar ce bayan shafe makwanni takwas ta na yakar mayakn Kurdawa na kungiyar YPG da ke take kallo a matsayin ‘yan ta’adda.

A halin da ake ciki, kungiyar bada agajin kasar Turkiya ta Red Crescent ta fara aikin rabawa fararen hular da ke yankin kayayyakin abinci yayinda sojoji ke cikin shirin ko ta kwana.

Gwamnatin Turkiya ta ce tun bayan barkewar yakin basasar kasar ta Syria a 2011 zuwa yanzu, ta bai wa ‘yan gudun hijirar Syria akalla miliyan uku da dubu dari biyar mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.